27 Faburairu 2021 - 08:42
​Iran Da Syria Sun Jaddada Wajabcin Ci Gaba Da Kara Karfafa Alaka Tsakaninsu A Dukkanin Bangarori

Gwamnatocin kasashen Iran da Syria sun jaddada wajabcin ci gaba da kara karfafa alaka a tsakaninsu a dukkanin bangarori.

ABNA24 : Wannan ya zo a wata zantawa da ta gudana a jiya tsakanin ministan harkokin wajen kasar Syria Faisal Miqdad, da kuma takwaransa na kasar Iran Muhammad Jawad Zarif.

Bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da suka shafi alaka a tsakanin kasashensu da kuma wajabcin ci gaba da kara bunkasa wannan alaka a dukkanin bangarori.

Baya ga haka kuam sun tattauna a kan wasu batutuwa da suka shafi yankin gabas ta tsakiya da kuma halin da ake ciki a yankin, da yadda za su ci gaba da yin hadin gwaiwa wajen tunkarar abubuwan da suke faruwa.

A daya bangaren kuma sun tattauna wasu batutuwa da suak shafi lamurra na kasa da kasa, da yadda a wannan bangaren ma za su ci gaba da yin hadin gwaiwa a tsakaninsu dangane da lamurra da suka hada su.

Haka nan kuma sun tattauna batun zaman Sochi na kasar Rasha, wanda aka gudanar karkashin shirin zaman lafiya na Astana, da nufin sansanta tsakanin gwamnatin Syria da kuma ‘yan adawar siyasa na kasar.

342/